Wednesday, 1 August 2018

Man United na neman Zidane

Manchester United tana son tsohon kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya maye Jose Mourinho idan ya tafi, in ji (Sun).


Wasu rahotanni sun ce Manchester na iya raba gari da Mourinho, kamar yadda kocin ya nuna alamun shi ma zai iya ajiye aikinsa.

Inter Milan na sha'awar sayen dan wasan tsakiyar Real Madrid dan kasar Croatia Luka Modric, mai shekara 32, wanda yake hutu a Italiya, in ji jaridar Gazzetta dello.

Chelsea na fatan doke Real Madrid wajen takarar sayen dan wasan Bayern Munich dan kasar Poland, Robert Lewandowski, mai shekara 29, in ji,(Star).
BBChausa

No comments:

Post a Comment