Sunday, 19 August 2018

Martanin Ganduje ga Kwankwaso: Ni na yarda mijin hajiyane,kai kuma mijin wacece?

A yayin da yake jagorantar tallafawa mata daga kananan hukumomin jihar Kano, Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya mayarwa da tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso martani bisa cemai da yayi mijin hajiya.


Gwamna Ganduje yace, ( Kwankwaso) ya tashi cikin jama'a yace ina matasan Kano? Idan kun koma ku gaishe da mijin hajiya, to ni mijin matata ne kuma tana sona ina sonta.

Gwamna Ganduje ya kara da cewa, kuma shi saboda ya san datajar mata, bazai aibanta matarshi ba, saboda kowa yasan ta fito ne daga gidan mutunci dan haka yana mata addu'ar Allah ya bata zuri'a ta gari, yasa Aljannace makomarta.

Yace, fadin mijin hajiya ma ai ba tozarci bane.

Amma shi ya yarda cewa shi mijin hajiyane, to shi(Kwankwaso) sai ya gaya mana shi mijin wanene?

No comments:

Post a Comment