Monday, 20 August 2018

Masoya Buhari dana Saraki sunyi gasar yabon gwanayensu a Ilori

Masoyan shugaban kasa, Muhammadu Buhari dana kakakin majalisar dattijai, Bukola Saraki sunyi gasar yiwa gwanayensu kirari a jihar Ilori lokacin da magoya bayan sukaje tarbar Sarakin da dan takarar gwamnan jihar a filin jirgin saman jihar, jiya Lahadi.


Masoya Buhari, sunje tarbar 'yan takarar gwamnan jihar, Mr Moddibo Kawu da Mr Issa Aremu, su kuma 'yan PDP sujene su tarbi Sanata Bukola Saraki, da farko dai komai kalau sai daga bayane masoya Saraki wanda mafi yawanci matane suka fara wakokin yabonshi, aikuwa suma masoya Buhari da sukaji, wanda mafi yawansu matasane sai suka dauki wakar Sai Baba suna daga tsintsiya.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, saida jami'an tsaro suka sa hannu sannan aka samu daidaito.

No comments:

Post a Comment