Friday, 31 August 2018

Mataimakin Ali Modu ya ankarar da Buhari tuggun da tsohon maigidan nasa ke kulla masa

Alhaji Shettima Yuguda Dibal ne mataimakin gwamna Ali Modu Sheriff na jihar Borno daga shekarar 2003 zuwa 2011 ya gargadi shugaba Muhammadu Buhari da shugaban jam'iyyar APC, kwamared Adams Oshiomhole a kan abinda ya bayyana a matsayin dabaru da damfara da Ali Modu Sherrif ko kokarin yiwa jam'iyyar APC.


A wata hira da Wazirin Biun ya yi da manema labarai a Abuja, ya ce ya cigaba da zama a jam'iyyar APC ne ko da yake gwamna Ali Modu Sherrif ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP domin ya san cewa talakawan jihar Borno APC su keyi hakan yasa PDP ba ta taba mulkar jihar ba.

Yuguda Dibal ya ce Sherrif shi a kullum kokarinsa shine ya rika yiwa shugaban kasa fadanci saboda ya rika biyan bukatunsa. Dibal ya ce Ali Modu Sherrif ya yi kokarin janyo hankalin sauran 'ya'yan jam'iyyar APC su biyo PDP amma basu amince ba.

Da yake tsokaci kan komowar Sherrif jam'iyyar APC, Yuguda Dibal ya ce tsohon gwamnan ya dawo APC me saboda bashi da wata zabi kuma domin yana son ya kusanci shugaban kasa Muhammadu Buhari don cimma wasu buri nasa na siyasa.

Tsohon mataimakin gwamnan kuma ya gargadi jam'iyyar APC tayi kafa-kafa da irin alkawurran da Ali Modu Sherrif ke dauka wanda kuma baya iya cikawa inda ya bayar da misalin yadda Sheriff ya yiwa tsohon shugaba Jonathan alkawarin kawo kuri'un Borno a 2015 amma Jonathan ya sha kaye.
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment