Monday, 6 August 2018

Mataimakin gwamnan Jihar Kano ya ajiye aikinshine saboda tsoron tsigeshi da ake shirin yi

A jiyane mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar ya ajiye mukaminshi inda ya bayyana rashin girmama ofishinshi da kuma rashin biyanshi hakkokinshi na alwus-alawus da kuma wulakanci da gwamnan ke mai a matsayin dalilai da suka sa ya ajiye muka min nashi, kamar yanda ya bayyana a takardar ajiye aikin daya mikawa gwamnan.


Saidai gwamnatin jihar Kanon ta musanta wadannan zarge-zarge nashi inda tace, Farfesa Hafiz yaji tsoron yunkurin tsigeshi da majalisar jihar Kano take yine shi yasa dan kada a kunyatashi yayi sauri ya ajiye aikin da kanshi.

Sanarwar wadda kwamishinan watsa labarai na jihar ya fitar tace, 30 cikin 40 na 'yan majalisar jihar sun riga sun amince da tsige mataimakin gwamnan bisa laifin yiwa gwamnatin jihar zagon kasa da kuma fitowa fili da yayi yace yana goyon bayan tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Haka kuma sanarwar ta musanta zargin da mataimakin gwamnan yayi na cewa ana barazana ga rayuwarshi, inda tace a matsayin shi na mutum na biyu a jihar yana da jami'an tsaro masu kula da lafiyarshi dan haka wannan zargine mara tushe.

Sanarwar ta kuma kara da cewa, an kashewa ofishin mataimakin gwamnan kudade da dama da suka hada da kudin da aka bashi na zuwa kasashen Ingila, Sudan da Saudiyya inda diyarshi zata kammala makaranta.

Sanarwar ta karkare da cewa, gwamnatin jihar Kano zata iya daukar matakin daya dace akan mataimakin gwamnan bisa wadannan zarge-zarge marasa tushe da ya mata saboda girmansu.

Ta kara da cewa, kamata yayi mataimakin gwamnan ya ajiye mukamin nashi salin-alin ba tare da yin zarge-zarge marasa tushe ba dan kawai ya dauki hankulan mutaneba.

No comments:

Post a Comment