Wednesday, 1 August 2018

Mataimakin gwamnan jihar Kano ya fita daga APC

Mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar, ya sauya sheka daga jam'iyyar All Progressives Congress APC zuwa jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party PDP.

Mataimakin gwamnan ya koma jam'iyyar PDP ne da yammacin yau Laraba, 1 ga watan Agusta 2018. Farfesa Hafiz ya dau wannan mataki ne bayan ya kawo kukan cewa wasu na kokarin daukan ransa.

Bayan wannan kuka, gwamnati ta kara masa jami'an tsaro domin karesa daga abinda yake tsoro.

Jam'iyyar PDP ta bayyana wannan labari a dandalinta na sada zumunta inda tace, 

" Mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar, ya fita daga jam'iyyar All Progressive Congress (APC), zuwa jam'iyyar PDP".

No comments:

Post a Comment