Thursday, 23 August 2018

Matashin da yayi tattaki lokacin da Buhari yaci zabe yace yayi dana sanin yin hakan

Mutuminnan da ya yi tattaki lokacin da jam'iyyar APC ta ci zabe a shekarar 2015 wanda aka bayyana da sunan Mukaila yace yayi da na sanin yin wancan tattaki saboda jam'iyyar ta APC bata cika alkawarin data dauka na samarwa matasa aikin yi ba.Matashin yace, saboda ya nuna bacin ranshi ya kama hanyar sake yin wani tattakin daga birnin Legas zuwa babban birnin tarayya Abuja kuma ya bar jam'iyyar ta APC kenan.

Saidai be bayyana ko wace jam'iyya zai koma ba ya zuwa yanzu, kamar yanda shafin naija.ng ya ruwaito.

Ya kuma kara da cewa ba wanine ya dauki nauyinshi yayi wannan abuba kuma bashi da wata alaka da siyasa, yana da kudinshi, shine yake daukar nauyin kanshi,kawai yana yine a matsayin wakilin matasan Najeriya.

No comments:

Post a Comment