Sunday, 19 August 2018

Messi ya ciwa Barcelona Kwallo ta 6000 a gasar Laliga

Tauraron dan kwallon kungiyar Barcelona, Lionel Messi ya ciwa Barca kwallo ta 6000 a gaba dayan kwallayen da taci tun da ta fara gasar Laliga, Messin yaci wannan kwallonne jiya, Asabar a wasan da suka buga da Alaves wanda ya tashi Barca na cin Alaves din 3-0.


Barcelona taci wadannan kwallaye 6000 a wasanni data buga guda 2801 tun daga shekarar 1929 data fara buga gasar Laliga.

Saidai Real Madrid tana gaba da Barca a yawan kwallaye inda yanzu Madrid din taci jimullar kwallaye 6041 kenan a wasanni 2800 data buga a gasar ta Laliga.

Bayan kwallon ta biyu da Coutinho ya ciwa Barcelona, Messi ya kara cin kwallonshi ta biyu wadda itace ta zama kwallonshi ta 385 a gasar ta Laliga.

Messin ne dai ya ciwa Barcelona kwallo ta 5000 a watan Fabrairu na shekarar 2009 a gasar ta Laliga kamar yanda ESPN ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment