Sunday, 19 August 2018

Minista ta rankaya asibiti a kan keke don ta haihu

Ministar harkokin mata a kasar New Zealand ta rankaya asibiti a kan keke domin ta yi haihuwarta ta fari.


Ta haihu ne bayan cikin nata ya kai mako 42.

Minista Julie Genter ta jam'iyyar The Green Party ta ce ta ruga asibitin ne a kan keke domin a taimaka mata ta haihu saboda "babu sarari a cikin motata".

Ta wallafa hotunanta tare da mijinta a Instagram rike da kekunansu.

A watan Yuni, Firayi Ministar kasar Jacinda Ardern ta zamo shugabar gwamnatin wata kasa ta biyu da ta haihu tana kan mulki. Dukkan matan biyu na zuwa asibitin Auckland City Hospital wanda kowa da kowa ke zuwa.

Ms Genter, mai shekara 38, wacce kuma take rike da mukamin ministar sufuri, ta yi fice wajen rajin hawa keke.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment