Monday, 20 August 2018

Modric, Ronaldo, Salah na takarar gwarzon Uefa

An bayyana sunayen Luka Modric, Cristiano Ronaldo da Mohamed Salah cikin jerin farko na 'yan wasan da ke takarar gwarzon dan wasan zakarun Turai, Uefa, na bana.


Kwamitin da ya kunshi alkalan wasa 80 da 'yan jarida 55 ne ya zabi dan wasan tsakiya na Real Madrid Modric, dan wasan gaba na Juventus Ronaldo da kuma dan wasan gaba na Liverpool Salah domin yin takarar.

Za a ba da kyautar gwarzon dan kwallon kafar ne lokacin da za a yi wasannin rukuni na gasar cin kofin zakarun Turai a Monaco ranar 30 ga watan Agusta.

An bayyana sunayen Pernille Harder, Ada Hegerberg da kuma Amandine Henry domin fafatawa don zama gwarzuwar 'yan kwallon kafar Uefa ta mata a bana.

'Yar wasan gaba ta Denmark Harder tana buga wa Wolfsburg wasa, yayin da 'yar wasan gaba ta Norway Hegerberg da 'yar wasan baya ta Faransa Henry ke buga wasa a Lyon.

Ronaldo, wanda ya koma Juventus daga Real Madrid a watan Yuli a kan £99.2m, ya taba lashe gasar a 2017, yayin da Lieke Martens ta lashe gasar jim kadan bayan ta koma Barcelona daga Rosengard.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment