Sunday, 5 August 2018

"Musulunci ya kubucewa larabawa"

Wani bidiyo da ke dauke da kalaman firaministan Habasha, Abi Ahmed ya haifar da zazzafan cece-kuce a shafuka sada zumunta da kafofin yada labarai na duniya.


A bidiyon an nuna Abi Ahmed a wani taron Musulmai Itopiya mazauna Amurka,inda yake cewa : "Yayin da na kai ziyara Hadaddiyar Daular Larabawa a makon da ya gabata,sarkin Musulmi na wannan kasar,Mohammed Bin Zayed ya nuna bukatarsa ta tallafa wa Habasha wajen gina cibiyyar Islamiyya da zummar koya mana Musulunci.Amma sai na amsa masa cewa,ba zaku (Larabawa) iya ba, don tuni ya Musulunci ya kubuce muku.Kuma kowa ya kalli halin da kasashen yankin Gulf ke ciki a yau, ya san cewa babu hadin-kai.Akwai darikun Musulunci da basu taba kawo gundunmowa wajen gina Islam ba.Akwai shiyyoyin Musulmai da ke ci gaba tarwatsa Musulunci".

Wadannan kalaman sun dinka yaduwa a shafukan intanet a cikin kiftawar ido,inda suka suka haifar sa-in-sa marar misaltuwa.

Kawo yanzu babu wata masaniya kan ko wannan bidiyo zai gurbata huldar da ke tsakanin kasashen biyu,amma tuni ministan harkokin wajen Habasha,Meles Alem ya bayyana gaban manema labarai don yin tsokaci kan wannan batun, inda ya ce:

"An yi wa kalaman Ahmed Abi mummunar fassara.Saboda bai ware wata kasa daya tak ba don nuna ma ta yatsa.Ya yi magana ne kan yadda karantarwar Islam kan zaman lafiya ya kubuce wa Musulmai.Alakar da ke tsakanin kasarmu da Hadaddiyar Daular Larabawa na da karfi sosai.Babu wani kalamin da zai gurbata ta".

Tun farkon watan Mayun ya zuwa yau,Abi Ahmed ya kai ziyara Hadaddiyar Daular Larabawa sau biyu,inda shugabannin kasar suka bai wa Habasha dalar Amurka biliyan 3 don bunkasa tattalin arzikinta.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment