Sunday, 5 August 2018

Na gwammace na bar siyasa dana bar jam'iyyar PDP>>Makarfi

Alhaji Ahmed Makarfi ya bayyana yiyuwar barin sa jam'iyar PDP idan bai samu damar samun tikitin zaben 2019.


Yace zai bar siyasa baki daya maimakon ya koma wata jam'iyar.

Makarfi ya bayyana haka ne a ranar Asabar yayin da yake ganawa da manema labarai a sakateriyar PDP dake Minna dake Jahar Niger

Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN, ya bayyana cewa Makarfi ya halarci Minna ne don neman goyan bayansu akan kujerar Shugaban kasa a 2019

Yace "Idan zanbar PDP to zanbar siyasa baki daya. Da ace zanbar PDP da tuntuni na bari to har yanzu babu damar barin".

"Wasu mutanen da an zungure su(ya taba kafadar sa) sai su koma wata jam'iyar a lokacin sai na dakata, ku kuma saiku karbesu a gidanku sannan ku basu dakin baki, daga baya saisu koma dakuna abu na karshe kuma sai su kore ku daga gidan naku, to mu bazamu kyale hakan ba kuma bazamu basu wannan damar ba saboda haka bazamu rarraba mutanen mu ba".

Makarfi yace zamubar Bakola Saraki akan kujerar sa ne saboda bai sabawa kundun tsarin mulki ba saboda barinshi APC zuwa PDP.

Makarfi dai tsohon gwamnan jahar Kaduna ne sannan yana rike da mukamin Ciyaman na PDP na kasa.

No comments:

Post a Comment