Tuesday, 28 August 2018

Na yi dana sanin goyon bayan Buhari>>Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma mai neman jam'iyyar PDP ta tsayar da shi takarar shugaban kasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya bayyana cewar shi da wasu jiga-jigan yan siyasa ada suka canja sheka daga PDP zuwa APC sun yi nadamar goywa shugaba Buhari baya a shekarar 2015.


Kwankwaso na wadannan kalamai ne a garin Owerri, babban birnin jihar Imo, inda ya ziyarci 'ya'yan jamiyyar PDP a cigaba da tubtubar da yake yi domin tsayawa taarar shugaban kasa.

Tsohon gwamnan ya nuna takaicinsa bisa irin rikon da shugaba Buhari ya yiwa tattalin arzikin Najeriya da kuma yadda ya wofantar da yankin kudu maso gabas na 'yan kabilar Igbo. Kazalika ya bayyana cewar canjin gwamnati ne kadai zai kawo gyara a yadda ake gudanar da al'amuran gwamati.

Kwankwaso ya nuna karfun gwuiwar sa a kan cewar jam'iyyar PDP zata lashe zaben shugaban kasa da kuma mafi yawan jihohin Najeriya.

A kalaman Kwankwaso, "daga arewa zuwa kudu, 'yan Najeriya na neman gwamnatin da zata inganta rayuwar su ba tare da la'akari da addini, kabila ko yankin da suka fito ba."

"Daga abinda na gani a nan yankin kudu maso gabas, a bayyana yake cewar gwamnati ba zata iya kawowa wannan yanki cigaba ba kuma ba zata iya inganta rayuwar su ba. An kasa inganta rayuwar mutanen yankin kuma an kasa inganta tattalin arzikin yankin. Mutane na bukatar gwamnatin da zata basu aiki tare da yi masu adalci," a kalaman Kwankwaso.

A jawabin shugaban jam'iyyar PDP na jihar Imo, wanda mataimakinsa, Martin Ehiogu, ya wakilta, ya bayyana cewar 'yan kabilar Igbo zasu zabi shugaban kasa ne da zai iya yiwa yiwa tsarin mulkin Najeriya garambawul.
Naija.ng.


No comments:

Post a Comment