Sunday, 19 August 2018

Najeriya na da bukatar shugaban da zai samarwa da mutane aikin yi: Ni kuma ina da kwarewa a wannan fannin>>Atiku

A ci gaba da rangadin da yake a jihohin Najeriya kamin zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP, tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci jihar Enugu inda ya bayyana cewa, Najeriya na da bukatar shugaban da zai samarwa da mutane aikin yi kuma shi din yana da kwarewa akan hakan.


DailyTrust ta ruwaito cewa, Atiku ya bayyana hakane ranar Alhamis din data gaba a Enugun inda yace , a yanzu Najeriya na fama da rashin aikin yi wanda kiyasi ya nuna kimanin mutane miliyan 12 ne suka rasa ayyukansu sannan wadanda ke aikin ba'a biyansu yanda ya kamata.

Wannan ya kara hura wutar matsalar tsaro a kasarnan injishi.

Yace a lokaci irin wannan, Najeriya na da bukatar wanda zai samawar wa da mutane aikin yi kuma shi yana da kwarewa a wannan fannin inda ya samarwa da mutane aiki a gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.

Atiku yayi kira ga 'yan Najeriya dasu yi kokari su samu katin zaben su sannan kuma su kada kuri'arsu su kuma kareta.

No comments:

Post a Comment