Saturday, 4 August 2018

Neymar ya taimaki PSG doke Monaco a gasar Super Cup

Neymar ya shiga wasan an kusa tashi, inda PSG ta doke Monaco 4 - 0 a gasar Super Cup.
Wasan na China shi ne karon farko da dan wasan dan asalin kasar Brazil ya buga ma PSG kwallo tun watan Fabrairu bayan ya sami rauni a kafarsa.


Neymar ya shiga wasan ne da misalin minti 75 a wasan da zakarun league 1 na Faransa suka kara da masu rike da kofin kasar na bara.

Angel Di Maria ne ya jefa kwallo biyu, shi kuma Christopher Nkunku da Timothy Weah suka jefa sauran kwallo biyun a ragar Monaco.

A gaban 'yan kallo 41,237 da ke cikin filin wasa na Shenzhen, dan wasan Argentina Di Maria ya jefa kwallo ta farko a minti na 32, daga nan kuma Nkunku da Weah - dan tsohon dan wasan PSG da AC Milan kuma shugabn kasar Liberia George Weah suka aika da kwallayensu.

Sabon kocin PSG Thomas Tuchel ya saka Neymar daga baya kafin Di Maria ya sake jefa wata kwallon, kuma wannan ya ba kungiyar nasara a karo na takwas kenan a gasar Super Cup ta Faransa.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment