Sunday, 12 August 2018

Ni ba irin Buhari bane: da yace sau daya zai yi mulki amma ya karya alkawari: Muddin na zama shugaban kasa to zan sanya hannu a takarda cewa zango daya zanyi>>Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Wazirin Adamawa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana irin yanda zai samarwa matasa aikinyi a kasarnan idan ya zama shugaban kasa a zaben 2019 me zuwa.


Yayi wannan maganane a wata hira da yayi da jaridar Thisday inda yace, a yanzu haka yana da mutane dubu 50 dake aiki a karkashinshi kuma sama da shekaru 4 kenan yana samarwa da mutane ayyuka na kai tsaye da wanda bana kai tsaye ba.

Ya kara da cewa kuma muddin ya samu damar zama shugaban kasa, sau daya kawai zaiyi mulki bazai kara ba.

Da aka tambayeshi wani zaice watakila yana fadin hakanne kawai dan ya samu wannan dama amma idan ya hau zai iya canjawa.

Sai yace, shi fa ba irin Buhari bane, da yawa 'Yan Najeriya irin wannan alkawarin amma ya kasa cikawa, shi zai sa hannu a takardar alkawarin cewa sau daya zai yi mulki.

No comments:

Post a Comment