Sunday, 12 August 2018

Nijeriya Za Ta Yi Babbar Sallah Rana Daya Da Saudiyya

Biyo bayan bada sanarwar ganin wata da kasar Saudiyya ta yi a yau Asabar, alhali mu a nan kasar muna 28 ne, wakilin RARIYA a Sokoto ya samu zantawa da Dr. Mansur Ibrahim Sokoto, inda ya shaida muna cewa lallai Saudiyya ta ga watan, kuma ya sanar da Mai martaba, yana tattaunawa da sauran malumma da sarakuna, daga karshe ga sakon da Dr. Ya izo. "Ganin Wata a Nijeriya.


Mai alfarma Sarkin Musulmi ya amince da yin Sallah a Najeriya tare da Saudia wato ranar Talata 21 ga Agusta 2018 bayan tuntubar manyan Malamai na kasa da Sarakuna.

Bisa ga haka, mutane suna iya fara azumin Dhul Hajji daga gobe lahadi.
A saurari sanarwa daga majalisar mai alfarma Sarkin Musulmi. Da kuma sharhi da zamu fitar daga baya in Allah ya so.

Mun sanar da ku ne don yawan wayoyi da ake ta bugowa daga ko ina ana tambaya. Allah ya karbi ibadarmu", inji Mansur Sokoto.

No comments:

Post a Comment