Tuesday, 7 August 2018

Osinbajo ya sauke shugaban 'yan sandan farin kaya, DSS, Lawal Daura daga mukaminshi

DSS DG
Da safiyar yau, Talata ne, jami'an 'yan sandan farin kaya na DSS suka tare kofar shiga majalisar inda suka hana wasu 'yan majalisar shiga gurin aikinsu, rahotanni dake fitowa sun tabbatar da sauke shugaban ma'aikatar DSS, Lawal Daura daga mukaminshi.Me baiwa mataimakin shugaban kasa kuma shugaban kasar riko, Farfesa Yemi Osinbajo shawara akan harkar watsa labarai, Laolu Akande ne ya bayyana haka ta dandalinshi na shafin twitter.

Sanarwar ta bayyana cewa shugaban kasar riko, Osinbajo ya bukaci Lawal Daura ya ajiye mukaminshi, ya baiwa ma'aikacin hukumar DSS mafi girman matsayi rikon mukamin kamin a fitar da sabuwar sanarwa.

No comments:

Post a Comment