Thursday, 23 August 2018

PDP ce zata ci zabe a 2019>>Saraki

Kakakin majalisar dattijai, Bukola Saraki ya bayyana cewa, jam'iyyarsu ta PDP ce zata samu nasara a zabukan shekarar 2019 dake tafe.


Saraki ya bayyana hakane a lokacin da yake ganawa da 'yan jam'iyyar daga kananan hukumomin jihar Kwara 16 da suka kaimai ziyara, ya bayyana cewa idan Allah ya yarda tun daga kan gwamnatin tarayya har kasa PDP ce zata ci zabe.

Saraki ya kuma bayyana cewa, bashi da wani dan takara da yake goyon baya, yace za'a zabi 'yan takarane ta hanyar amincewar mutane dan samun shuwagabanni na gari.

No comments:

Post a Comment