Thursday, 9 August 2018

Pogba ya nemi Man U ta kara mai albashin, in ba haka ba zai koma Barcelona

Jaridun Birtaniya sun rawaito cewa, dan wasan Faransa da ya nuna bajintarsa a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a Rasha, wato Paul Pogba ya tsayar da shawarar kawo karshen tankiyar da ke tsakaninsa da kocin kungiyarsa ta Manchester United, Jose Mourinho, in da zai koma Barcelona da murza leda.


Pogba wanda ya zura kwallo a wasan karshe da Faransa ta doke Croatia da ci 4-2 a gasar ta cin kofin duniyar, ya amince da kulla kwantiragi da Barcelona akan farashin fam miliyan 89.5, kwatankwacin Dala miliyan 115.

Jaridar Daily Mail ta ce, Pogba zai kulla kwantiragin ne na tsawon shekaru biyar, in da zai rika karbar albashin Pam dubu 346 a kowanne mako, kwatankwacin Nairar Najeriya, miliyan 16 da doriya, kudin da ya kusan ninka albashinsa a Manchester United.

Jaridar Sun ta rawaito cewa, Pogba ya bukaci Manchester United da ta kara masa albashinsa a kowanne mako daga Pam dubu 180 zuwa Pam dubu 380 ko kuma ya raba gari da ita.

Sai dai ana ganin mawuyaci ne Manchester United ta sayar da Pogba wanda ta sayo daga Juventus akan Pam miliyan 89 a shekarar 2016 daga Juventus.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment