Wednesday, 8 August 2018

Rahama Sadau ta bude kamfanin yin Jan Baki

Tauraruwar fina-finan Hausa da turanci, Rahama Sadau ta bude kamfanin yin abin kwalliyar mata na jan baki, kamar yanda ta bayyana, 'yan uwanta matane suka bijiro da wannan tunani, ita kuma tayi kokarin ganin ya tabbata da taimakon Allah sannan da wasu abokan aikinta da suka bayar da nasu gudummuwar.Damai Rahamar nada kamfanin Sadau Pictures wanda tun a baya ta budeshi.

Rahama ta bayyana cewa nan bada dadewa ba jam bakin zai shiga kasuwa a fara sayar dashi.

Muna tayata murna da fatan Allah ya kawo kasuwa

No comments:

Post a Comment