Wednesday, 15 August 2018

Ramos ya caccaki Ronaldo da Klopp

Tauraron dan kwallon kafar kungiyar Real Madrid, Sergio Ramos ya caccaki tsohon abokin wasanshi, Cristiano Ronaldo saboda wata magana da Ronaldon yayi bayan komawarshi Juventus.


The Mirror ta Uk ta ruwaito cewa, Ronaldo yace, yafi jin dadin zama a sabuwar kungiyarshi ta Juventus fiye da tsohuwar kungiyarshi ta Real Madrid domin yanda suka zama kamar 'yan gida daya.

A martaninshi, Ramos yace, Real Madrid fa tafi karfin wani dan wasa guda daya kuma nasarorin da Ronaldo ya samu a kungiyar ta duka 'yan wasanne domin sunyi aiki tare wajan samunta.

Yace tabbas, Rashin dan wasa irin Ronaldo abin takaicine amma fa 'yan wasa da dama sunzo kungiyar sun tafi kuma kungiyar taci gaba da samun nasara dan haka wannan karinma abinda zai faru kenan.

A wani labarin kuma Rmos din dai ya caccaki me horas da 'yan wasa na kungiyar Liverpool, Jurgen Klopp akan maganar karanbattar da Ramos din yayi da Mohamed Salah a wasan karshe na cin kofin zakarun turai wanda yayi sanadin karyewar hannun Salah din.

Ramos yace, ya kamata Klopp ya ji da abinda ke damunshi ya kuma bari maganar ta wuce, ya kara da cewa bafa wannane karin farko da Klopp din ke rashin nasara wasan karsheba, dan haka ya daina danganta abinda ya faru tsakaninshi da Salah da rashin nasarar da yayi.

Yace, shidai ya riga ya fadi tun a baya cewa, Salah ne ya sarkafa hannunshi a hamatarshi kuma abinda ya faru ba da gangan bane.

No comments:

Post a Comment