Monday, 20 August 2018

Rashin Cristiano Ronaldo ya kawo karancin 'yan kallo a filin Real Madrid

Masu kallo basu cika filin wasan Real Madrid ba yanda aka saba lokacin Cristiano Ronaldo na nan ba a wasan da suka buga jiya ga Getafe wanda ya kare Madrid din na cim 2-0.


Carjaval da Bale ne suka ciwa Madrid kwallayen biyun,to amma duk da sunyi nasara a wasan, abinda ya dauki hankulan mutane shine rashin 'yan kallo da basu cika filin na Santiago Bernabeu ba.

'Yan kallo 48,466 ne kawai suka shiga filin a jiya yayin da aka ga kujeru da yawa babu mutane a filin, kamar yanda Goal ta ruwaito, wannan dai shine mafi karancin 'yan kallo da suka je kallon wasan na Real Madrid a cikin shekaru 10 da suka gabata, tun kamin zuwan Ronaldo kungiyar.

Lokaci na karshe da Madrid ta samu karancin 'yan kallo irin wannan shine tun wasan karshe na shekarar 2008-9 da suka buga El-clasico da Barcelona, a wancan lokacin Thierry Henry da Lionel Messi sukaci kwallaye biyu kowannensu wanda wasan ya kare Barca na cin Madrid 6-2.

Daga nan ne suka sayo Ronaldo a shekarar 2009.

Wannan dai shine wasan Madrid din na gasar Laliga na farko tun bayan tafiyar Ronaldo kuma da dama sun alakanta rashin Ronaldo da karancin 'yan kallon da aka samu, saidai masu sharhi na ganin cewa idan Madrid din ta ci gaba da samun nasara a wasannin ta na gaba, watakila 'yan kallon zasu karu.

No comments:

Post a Comment