Friday, 24 August 2018

Real Madrid zata sayi Kylian Mbappe idan...

Hukumar kula da kwallon kafa ta Duniya, FIFA na duba yiyuwar sakawa kungiyar kwallon kafa ta PSG takunkumi akan karya dokar kashe kudi da suka wuce kima wajan sayen 'yan wasa da albashin ma'aikata.


Idan FIFA din ta sakawa PSG wannan takunkumi zai zama dole a gareta ta sayar da daya daga cikin shahararrun 'yan kwallon ta. Lokacin aron Kylian Mbappe da suka amso daga Monaco zai kare ranar Litinin wanda zasu hadu da zabin kodai su sayi dan wasan akan kudi Yuro miliyan 180 wanda zaisa su kara karya wata dokar ta kashe kudi fiye da kima ko kuma su mayarwa da Monacon da shi, kamar yanda AS ta ruwaito.

Idan dai FIFA ta kakabawa PSG wannan takunkumi, to kungiyar Real Madrid ce ake tunanin zasu sayi dan wasan domin kuwa kasuwannin cinikin 'yan wasa a Ingila da Italiya duk a kulle suke.

Wannan zai baiwa Madrid din damar maye gurbin Cristiano Ronaldo da ta rasa.

No comments:

Post a Comment