Thursday, 23 August 2018

Ronaldo ya bayyana dalilin da yasa ya koma Juventus

Tauraron dan kwallo, Cristiano Ronaldo da ya koma kungiyar Juventus daga Real Madrid akan kudi Yuro Miliyan 100, ya bayyana dalilin da yasa ya koma Juve din.


Ronaldo wanda yaci kofin Champions League har sau 4 tare da Real Madrid da kuma sau daya da Manchester United, ya bayyana cewa, yana so yaci kofin tare da sabuwar kungiyarshi ta Juve.

Ya bayyanawa manema labarai hakane a lokacin da ya zama jakadan wani kamfani me suna DAZN, Ronaldo ya kara da cewa zasu mayar da hankali shi da abokan wasanshi dan ganin sunci kofin na Champions League, zata iya yiyuwa wannan shekararne ko kuma me zuwa ko kuma ta gabanta.

Da aka tambayeshi game da danshi, ko yana so ya gajeshi?, sai yace, shima yana da son shiga gasa, kamar shi yake lokacin yana yaro, ba ya son rashin nasara.

Ya kara da cewa, zai zama kamarni, ina da tabbacin haka, zan koya mishi wasu abebadai amma zai zabi abinda yake son yayi kuma zan goyi bayanshi akan abinda yake so.

Saidai yace, zai so dan nashi ya zama dan kwallo dan kuwa yana son yin kwallo.

No comments:

Post a Comment