Thursday, 16 August 2018

Rukayya Dawayya ta caccaki wata sabuwar jaruma da ta ce bata santa ba

Tauraruwar fina-finan Hausa, Rukayya Dawayya ta fito ta dandalinta na sada zumunta da muhawara ta caccaki wata abokiyar aikin ta da tace bata santa ba.


Rukayya bata bayyana ko da wa take ba, tace dai watace ta bata haushi.

A cikin bayanin nata tace duk wadda ta shigo masana'antar fim din Hausa daga shekaru 10 zuwa yanzu, su ta gani ta shigo.

Ga cikakke bayanin nata kamar haka:

"Bude idonki sosai ki ganni. karyane kice kina masana antar kannywood baki sanni bah. kokice bakisan sunana bah wlh karya kike. daga 10 years zuwa yanzu duk wacce ta shigo industry mutagani tashigo. idan kinzo da Alkhairi kiga Alkhairi idan kinshigo da sharri ko kwadayi duk kigani a kwaryar shanki. karyar banza­čś×. sorry my fan's wata banzace tabani haushi."

No comments:

Post a Comment