Tuesday, 7 August 2018

Sai da na roki ‘yan majalisar Kano don kada su tsige mataimaki na, amma ya watsa min kasa a ido

Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa shi ne ya roki ‘yan majalisar jihar kada su tube tsohon mataimakin gwamnan.


Hakan ya fito ne a cikin wata takarda da gwamnan ya aikewa da tsohon mataimakin nasa.

Tsohon mataimakin gwamnan Farfesa Hafiz Abubakar dai ya bayyana cewa ya ajiye mukamin nasa ne saboda rashin fahimta da suke samu a tsakaninsa da gwamnan.

Sai dai Gandujen ya musanta zargin da ake na rashin martaba ofishin mataimakin gwamnan.

Gwamnan ya ce "Idan zaka iya tunawa ni ne wanda na hana ‘yan majalisa tsige ka duk da cewar sun sanya hannu wajen ganin an cireka daga ofishinka".

Gwamnan ya kara da cewa duk da Faefesan ya ajiye mukamin nasa yana masa fatan alheri da kuma girmama hukuncin nasa da ya dauka.

Dama dai Hafiz Abubakar magoyin bayan Kwankwanso ne wanda shi ma suka dauki tsawon lokaci suna dauki ba dadi da gwamna mai ci.

A shekara ta 2014 ne Kwankwanso ya dauko Hafiz Abubakar daga Jami'ar Bayero dake Kano ya kawo shi cikin siyasa a matsayin wanda zai yiwa Gandujen mataimaki.


No comments:

Post a Comment