Sunday, 12 August 2018

Salah ya ci kwallo 1, ya rungumi yaron da ya shigo fili a wasan da liverpool ta lallasa West Ham da ci 4-0

Tauraron dan kwallon kafar kungiyar Liverpool Mohamed Salah ya fara buga gasar firimiya da kafar dama inda a wasansu da West ham wanda ya kare Liverpool na cin 4-0 ya zura kwallo daya a raga.
Sadio Mane ne yaci kwallaye 2 sannan Sturridge yci kwallo ta 4.

Ana tsaka da wasa wani karamin yaro masoyin Salah ya shammaci jami'an tsaro ya shigo fili da gudu, yana shiga filin, beyi wata-wata ba yayi kam Salah inda ya rungumeshi.

Shima Salah din cikin farin ciki ya tarbi yaron inda daga baya ya takashi wajen fili kamin aka ci gaba da wasa.

Salah dai dama yana da yanayin fara'a da kuma rashin shariya.

No comments:

Post a Comment