Tuesday, 28 August 2018

Salah ya zargi hukumar kwallon kafar Masar da kin kulawa da koke

 Dan wasan gaban Liverpool da Masar, Mohamed Salah, ya zargi hukumar kwallon kafar Masar (EFA) kan kin kulawa da koke-kokensa kan hakkin hoton talla.


Salah, mai shekara 26, ya ji takaicin cewar an yi amfani da hotonsa a watan Afrilu wajen tallata kamfanin waya na WE mai daukar nauyin hukumar, yayin da yake da yarjejeniyar talla da abokin gogayyan kamfanin, Vodafone.

Hukumar ta musantata maganganun da ke cewa Salah ya ki buga wasan Masar da Nijar na watan Satumba saboda matsalar.

"An ki kula lauyoyi na da wasikuna," Kamar yadda Salah wallafa a wani sakon Twitter.

"Ban san me ya sa hakan ta faru ba. Shin ba ku da isasshen lokacin ba mu amsa ne?
"A bisa al'ada dai ko wace hukumar kwallon kafa tana kokarin warware matsalolin 'yan wasanta... amma hakikar abin da nake gani kishiyar hakan ne."

Lauyan Salah Ramy Abbas ya ce: "Mun nemi tabbaci game da lafiyar Mohamed yayin da yake tare da tawagar kwallon kafa ta kasa, da kuma tabbacin cewar ba za a sake take hakkin hoton tallanasa ba. Shi kenan. Kawo yanzu ba su mayar da martani ba."

Masar za ta kara da Nijar a wani wasan neman shiga gasar kofin Afrika ta shekarar 2019 ranar 8 ga watan Satumba.

Mai magana da yuwun hukumar EFA ya ce babu kanshin gaskiya a rahotannin da ke cewa Salah ka iya rasa damar buga wasan.


No comments:

Post a Comment