Sunday, 26 August 2018

Sanata John McCain na Amurka ya mutu

John McCain, wanda tsohon sojan Amurka ne wanda daga baya ya zama sanata, ya kuma tsaya takarar shugabancin Amurka ya mutu yana da shekara 81.


Mista McCain ya mutu ne a jiya Asabar kamar yadda wata sanarwa da ta fito daga ofishinsa ta bayyana.

Iyalan gidansa na tare da shi a lokacin da ya cika.

Likitoci sun gano cewa yana da wani tsiro a cikin kwakwalwarsa tun a watan Yulin 2017, kuma tun wancan lokacin yake karbar magani.

Iyalansa sun bayyana cewa ya yanke shawarar daina shan maganin ne a ranar Jumma'a, kuma rabonsa da zuwa aiki a birnin Washington tun watan Disambar bara.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment