Sunday, 26 August 2018

Sanata MacCain yabar wasiyyar kada Trump yazo kan gawarshi

Sanata John MacCain na kasar Amurka da ya mutu jiya, Asabar ya bar wasiyyar cewa kada shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya zo kan gawarshi ko kuma ya yi jawabi a gurin jana'izarshi.


Andai gayyaci tsaffin shuwagabannin kasar, Barrack Obama da kuma George W. Bush su gabatar da jawabi a gurin jana'izar ta tsohon sanatan,kamar yanda jaridar New York Times ta ruwaito.


Donald Trump dai na cikin wadanda suka mika ta'aziyyar marigayin a jiya, ta hanyar shafinshi na Twitter.

Tun kamin mutuwarshine, sanata MacCain ya bar wasiyyar cewa kada shugaban kasar yazo wajan jana'izarshi saboda irin rashin jituwar dake tsakansu.

No comments:

Post a Comment