Sunday, 19 August 2018

'Saraki ya yaudari Tambuwal: Bayan daya tunzurashi ya fito takarar shugaban kasa da alkawarin zai goyi bayanshi, shima yanzu neman takarar yake'

Wata majiya me karfi daga jam'iyyar PDP ta bayyana cewa, gwigwar gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal tayi sanyi da jin labarin cewa, kakakin majalisar dattijai, Bukola Saraki zai tsaya takarar shugaban kasa bayan Sarakin ya mishi alkawarin zai goya mishi baya.


Bayan komawarshi PDP, saraki ya bayyana cewa, yana nan yana neman shawarar mutane da masana akan tsayawa takarar shugabancin kasarnan a zaben shekarar 2019 me zuwa.

Idan dai Sarkin ya fito takarar to zai kasance na 11 dake neman tikitin jam'iyyar PDP na tsayawa takarar shugaban kasa dan kayar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Majiyar ta jaridar Thenation ta tabbatar da cewa, tun suna jam'iyyar APC Saraki yawa Tambuwal Alkawarin cewa idan ya fito takarar shugaban kasa zai goya mishi baya amma yanzu ya yaudareshi.

Majiyar tace, wannan tabbaci da Saraki ya baiwa Tambuwal na daga cikin abinda ya kara mai kwarin gwiwar fitowa takarar shugaban kasar.

Thenation tace, majiyar ta bayyana mata cewa yawan masu neman tikitin takarar shugaban kasar ya fara damunta. Saidai me magana da yawun jam'iyyar ta PDP, Kola Ologbondiyan ya bayyanawa jaridar cewa, Yawan 'yan takarar ba matsala bane dan kuwa sun koyi darasi a zaben da suka fadi na shekarar 2015, ba zasu yi magudi ba, zasu gudanar da zaben fidda gwani wanda kowane dan takara zaiyi na'am dashi.


No comments:

Post a Comment