Saturday, 25 August 2018

Sati me zuwa kwankwaso zai kaddamar da tsaya takarar shugaban kasa

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai kaddamar da tsayawa takarar shugaban kasa a ranar Laraba ta mako me zuwa idan Allah ya kaimu.


Jaridar Rariya ta bayyana haka a wani rahoto da ta wallafa.

Kwankwaso dai ya koma jam'iyyar PDP daga APC a kwanakin baya kuma akwai takun saka tsakaninshi da gwamnan jihar Kano me ci wanda kuma tsohon mataimakinshine, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Tun  bayan komawarshi PDP an samu rahotannin yimai ehon sai Buhari a lokuta daban-daban da ya shiga cikin mutane.

No comments:

Post a Comment