Sunday, 5 August 2018

Sati me zuwa Sanata Godswill Akpabio na PDP zai koma APC

Babban mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin da suka shafi majalisar dattijai, Ita Enang, ya tabbatar da dawowar tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio, zuwa jam’iyyar APC daga jam’iyyar PDP.


Enang ya sanar da hakan ne a jiya, Asabar, a shafinsa na Tuwita tare da bayyana cewar za a yi bikin karbarsa ranar 8 ga watan Agusta a jiharsa ta Akwa Ibom.

“Ina mai tabbatar da tabbatarwa da jam’iyyar APC cewar, kamar yadda muka bayyana a baya, za a karbi Godswill Akpabio zuwa APC a ranar 8 ga watan Agusta a jihar Akwa Ibom”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

An dade ana jitar-jitar cewar tsohon gwamnan zai koma jam’iyyar APC musamman ganin yadda ya cigaba da kauracewa taron jam’iyyar PDP.

A daren ranar juma’a ne wani jigo a PDP ya shaidawa jaridar The Nation cewar jam’iyyar ta aike da wakilci domin rokon shi a kan kada ya fita “amma ba zamu iya batawa gwamnan jihar, Udom Emmanuel, domin mu faranta masa ba saboda gwamna shine jagoran jam’iyya a jiha.”

Akpabio ya yanke shawarar fita daga PDP tun ranar 24 ga watan Yuli amma sai shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya ki sanar da majalisa saboda wasu dalilan siyasa.

Tun bayan wannan lokacin ya fara nuna alamun ya bar PDP ta hanyar kin halartar taron jam’iyyar har wanda aka shirya domin karbar wadanda suka fita daga APC da suka hada har da Saraki da Aminu Waziri Tambuwal na Sokoto, da gwamna Samuel Ortom na Benuwe, da sauran su.

No comments:

Post a Comment