Friday, 10 August 2018

Sau 6 Ronaldo ke cin abinci kullun, baya shan giya, baya shan siga

Dan kwallon kungiyar Juventus, Douglas Costa ya bayyanawa wani gidan talabijin na kasar Italiya a wata hira da sukayi dashi abin mamakin da ya gani tattare Cristiano Ronaldo.


Sky Italia ta ruwaito Costa na cewa, kullun idan suka zo yin atisaye suna iske Ronaldo ya rigasu zuwa haka kuma idan an tashi a nan suke barinshi yana motsa jiki, Costa yace sam ba zai iya bin Ronaldo su motsa jiki tare ba, duk da cewa Ronaldon ya girmeshi da shekaru 6.

Sau 6 Ronaldo ke cin abinci a kowace rana, yana kuma yawan shan ruwa amma baya shan giya kuma yana yawan cin ganye sannan baya cin abubuwan zaki, Costa yace wannanne yasa Ronaldo yayi zarra a Duniyar kwallo.

Ya kara da cewa, Ronaldo ya riga ya kai kololuwar samun nasara a harkar kwallon kafa amma irin motsa jikin da yake yi yanzu yana nuna cewa har yanzu yana son ya sake cimma wata nasara a rayuwarshi.

Ya kuma ce Ronaldon na da duk abinda ake bukata dan taimaka musu kaiwa ga tudun mun tsira a kakar wasan da za'a fara.

Mahaifin Ronaldo dai, José Dinis Aveiro, ya mutu a shekarar 2005 sanadin rashin lafiyar da ta kamashi saboda yawan shan giya, wasu na ganin cewa wannan ya hana Ronaldo bin sahun babanshi wajan shan giya.

No comments:

Post a Comment