Friday, 3 August 2018

SAUYA SHEKA: Allah Zai Ci Gaba Da Tsame Bara-Gurbin Dake Cikinmu>>Shugaba Buhari

SAUYA SHEKA: Allah Zai Ci Gaba Da Tsame Bara-Gurbin Dake Cikinmu, Inji Shugaba Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana masu sauya sheka daga APC zuwa wata jam'iyyar a matsayin bara-gurbi, inda ya yi fatan Allah zai ci gaba da tsame su daga ciminsu.


Shugaba Buhari wanda ya bayyana hakan a jiya Alhamis a garin Bauchi, ya kuma kara da cewa kada magoyan bayan APC su girgiza kan sauya shekar da ake yi a cikin jam'iyyar.

Kimanin gwamnoni uku ne dai wato na Benue, Kwara da Sokoto da wasu sanaroci da 'yan majalisu da kuma wasu jiga-jigan jam'iyyar ta APC suka sauya sheka zuwa PDP a kwanan nan.

Shugaba Buhari ya kara da cewa "ayyukan da muke yi muna yi ne saboda Allah da ku da kuma kasa. Ina so na tabbatar muku da cewa darrusan da muka dauka a baya ba za mu bari a sake cutar ku ba.

"Kamar yadda muka yi alkawari, abin da zai samar da ingatacciyar kasa a gaba sune tsaro, kwakkwaran tattalin arziki da kuma kawar da cin hanci da rashawa.

"Mun yi yakin neman zabe da wadannan kudirorin, kuma kuka zabe mu, don haka ba za mu manta ba", kamar yadda shugaba Buhari ya bayyana a gaban dubban magoya bayan jam'iyyar ta APC a yayin gabatar da dan takarar Sanata na Bauchi ta Kudu a filin wasa na Sir Abubakar Tafawa Balewa dake jihar Bauchi.

Shugaba Buhari ya kuma kara da tabbatarwa da magoya bayan jam'iyyar ta APC cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da aiki tukuru domin cika alkawurran da suka dauka a yayin yakin neman zabe don ganin Nijeriya ta kai ga samun nasara.

No comments:

Post a Comment