Tuesday, 7 August 2018

Shaidan ya shiga tsakanin Trump da matarsa Melania

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya samu matsala da matarsa Melania Trump saboda shahararren dan wasan kwallon kwando LeBron James.


Uwargidan Trump Melania ya yabi dan wasan LeBron James awanni kadan bayan mijinta ya zazzage shi ta shafinsa na Twitter.

A wata tattaunawa da James ya yi da kafar yada labarai ta CNN ya bayyana cewa, Trump na raba kan Amurkawa kuma yanayin siyasa ta nuna wariya.

Bayan hakan ne sai Trump ya fitar da sako ta shafin Twitter cewa,  ai mutumin da ya yi wannan tattaunawa a madadin CNN banza ne kuma shashasha.

Ya ce, an nuna james a matsayin mai tunani wanda wannan ba abu ne mai sauki ba.

Trump ya tuhumi kyawun hankali da tunanin James a sakon nasa ta shafin Twitter.

Awanni kadan bayan wannan kalami na Trump sai matarsa Melania ta bakin kakakinta ta nuna yabo ga james kan wani aikin gina makaranta da ya ke yi a Ohio.

Kakakin ya ma bayyana wa CNN cewa, nan da wani lokaci Melania za ta iya ziyartar makarantar.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment