Friday, 10 August 2018

Shehin Malami Ya Zama Kwamishinan 'Yan Sanda Na jihar Kaduna

Wannan da kuke gani a hoto shine sabon Kwamishinan 'yan sanda na jihar Kaduna Ash-sheikh AbdurRahman Ahmad (CP) HafizahulLahu Ta'ala.


CP Abdurrahman Ahmad Hafizi ne Mahaddacin Al-Qur'ani Maigirma, Mahaddacin Qur'ani ne gangaran tafsiran wa tajwidan, yana da haddar Qur'ani gaba daya a kansa, Malamin addinin musulunci ne masani mai tafsirin Al-Qur'ani Maigirma

Bayan kasancewarsa Malami Mahaddacin Qur'ani; a fagen aikinsa na tsaro kwararren jami'in 'dan sanda ne mai gaskiya da adalci, daga lokacin da ya fara aiki a Kaduna a matsayin kwamishinan 'yan sanda ya kawo gyara mai ma'ana da tsaftace jami'an 'yan sanda wajen hukunta duk wani jami'i da yake aiki ba bisa gaskiya da ka'idar aiki ba

Yanzu a Kaduna duk wani jami'in 'dan sanda da ya aikata ba daidai ba ya gwammace ace IGP ne yake kiransa ba wannan ba, saboda baya ragawa miyagu batagarin jami'ai masu karban cin hanci da rashawa, domin sakamakonsu kora ne daga aiki
Shiyasa yanzu haka batagarin 'yan sanda wadanda suke gudanar da aikinsu ba akan gaskiya da adalci ba suna batawa aikin suna a jihar Kaduna suna ta neman transfer suna guduwa

Haka muke fata Allah (SWT) Ya cigaba da samar mana jami'an 'yan sanda masu gaskiya da rikon amana wadanda suka san makamar aiki ba jahilai batagari ba

Muna rokon Allah Ya kara albarka a rayuwar Sheikh CP Abdurrahman Ahmad.

Allah Ya tsare mana shi Ya daukaka darajarsa Allah Ya kai mana shi matsayin IGP. Amin.
Rariya.

No comments:

Post a Comment