Saturday, 4 August 2018

Shugaba Buhari zai ba kowane 'Dan majalisa na APC N150m domin tsige Saraki da Dogara>>Timi Frank

Wani rahoto da sanadin shafin jaridar Vanguard ya bayyana cewa, fadar shugaban kasa da kuma shugabancin jam'iyyar APC, sun daura damarar tunbuke shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki da kuma kakakin majalisar wakilai, Honarabul Yakubu Dogara daga kujerun su.


Kamar dai yadda tsohon mataimakin kakakin jam'iyyar APC na kasa ya bayyana, Kwamared Timi Frank ya na zargi gami tuhumar fadar shuaban kasa da kuma shugabancin jam'iyyar APC, akan kulla tuggu da makircin tumbuke shugabannin majalisun biyu daga mukaman su.

Timi Frank dai ya bayyana cewa, fadar ta shugaban kasa da shugabancin jam'iyyar APC, na yunkurin bayar da cin hanci makudan kudade ga kowane dan majalisa na APC domin juyawa shugabannin majalisun su baya.

Tsohon kakakin ya fasa wannan tulu ne yayin ganawa da manema labarai cikin babban birnin kasar nan na Abuja a ranar Asabar ta yau, inda ya jeranto wasu gwamnonin da fadar shugaban kasa da kuma jam'iyyar ta APC ke kulla tuggun tumbuke su daga kujerun su.

Jaridar ta Vanguard ta bayyana sunayen wannan gwamnoni kamar haka; gwamna Aminu Waziri Tambuwa na jihar Sakkwato, gwamna Abdulfatah Ahmed na jihar Kwara da kuma Samuel Ortom na jihar Benuwe.

A yayin da ake shirya wannan tuggu na tsige Saraki da wannan Gwamnoni sakamakon raba gari da suka yi da jam'iyyar APC kuma suka koma jam'iyyar adawa ta PDP, ana kuma yunkurin tsige Dogara sakamakon fargaba ta ficewar sa daga jam'iyyar.Frank yake cewa daga sahihiyar majiya, fadar shugaban kasa tare da hadin gwiwar shugabancin jam'iyyar APC na yunkurin bayar da cin hancin $400,000, kimanin Naira miliyan 150 kenan ga sanatoci da mambobin majalisar wakilai na APC domin tsige Saraki da Dogara daga kujerun su.

Kazalika Timi ya ci gaba da cewa, za a baiwa 'yan majalisun dokoki na jihohi cin hancin na $150,000, kimanin Naira Miliyan 50 kenan domin tsige gwamnonin jihohin su da suka sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP.

Ya kuma kara da cewa, daf da tafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa birnin Landan a ranar Juma'ar da ta gabata, ya umarci shugabancin kamfanin man fetur na kasa watau NNPC, akan ya tanadi wannan makudan kudi domin cimma manufa ta tsige wadanda suka sauya sheka daga kujerun su.


No comments:

Post a Comment