Friday, 3 August 2018

Shugaban Marasa Rinjaye Na Majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio, Na Shirin Sauya Sheka Daga Jam'iyar PDP Zuwa APC

Jiya Alhamis mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, yayi wata ganawa da Shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio. 


Rahotanni sun bayyana cewar ganawar anyita ne domin cimma matsaya akan yiwuwar komawar Senata Akpabio jam'iyar APC daga jam'iyar PDP. 

Godswill Akpabio, tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom kuma jigo a jam'iyar PDP, ya kauracewa zaman masu ruwa da tsaki na jam'iyar PDP da aka gudanar jiya a sakatariyar jam'iyar PDP dake birnin tarayya Abuja, inda ya halarci ganawar sa da mataimakin Shugaban kasa akan cimma daidaito na yiwuwar ficewar sa daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC.
rariya.

No comments:

Post a Comment