Friday, 31 August 2018

Shugabar gwamnatin Jamus ta iso Najeriya

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta iso Abuja babban birnin Najeriya inda za su tattauna da shugaba Muhammad Buhari.


Ita ce shugaba ta biyu a nahiyar turai da ta kawo ziyara kasar don karfafa huldar kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

Kamar misis Theresa May, ita ma Merkel na tafe ne da tawagar 'yan kasuwar Jamus, amma akwai yiwuwar za su tattauna kan batun kwararan 'yan ci-ranin Afirka da batun zaben shugaban kasar da ke tafe a shekara mai zuwa.

Merkel na kawo ziyarar ne bayan zuwan shugaban Faransa Emmanuel Macron a watan Yuli, sai kuma Firministar Birtaniya da ta bar kasar ranar laraba.

Kusan dukkan shugabannin kasashen turan baututuwa guda ya kawo su, wato kasuwanci da tsaro da batun 'yan ci-rani.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment