Thursday, 9 August 2018

Stan Kroenke ya mallaki kungiyar Arsenal

An bayyana cewar shahararren attajiri mai suna Stan Kroenke ɗan ƙasar Amurka ya saye dukkanin hannayen jarin kungiyar kwallon ƙafar Arsenal.


Kronenke ya saye sauran hannayen jari kaso 30 cikin ɗari da wasu ke mallaka da zunzurutun kudi dala miliyan 714.

Stan Kroenke ya fara sayan hannayen jarin kungiyar ne a shekarar 2007 da kashi goma.

Bayan saukar Arsene Wenger wanda ya kwashe shekaru 22 ya na kochin kungiyar an nada Unai Emery a matsayin sabon kochin watanni uku da suka gabata.

Magoya bayan kungiyar na cikin fargaba ganin yadda ya rage kwanaki uku kafin fara wasan Premier league gasar da ta lashe tun a shekarar 2004.

A gasar bara ta kasance ta shidda, zata dai fafata da Manchester City a ranar Lahadi a wasan ta na farko a wannan karon.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment