Tuesday, 7 August 2018

Sule Lamido Ne Zai Iya Kai Nijeriya Ga Nasara>>Obasanjo

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana Sule Lamido da cewa zai iya shugabancin Nijeriya kuma zai iya abinda ake bukatar a yi, ya bayyana hakan yayin da Sule Lamido ya jagoranci tawagar yak'in neman zabensa domin ziyarar tattaunawa, bada bayanin zagayawa da tuntub'a neman adduo'i da kuma shawara irinta uba da d'a wadda suka kai masa a harabar ofishinsa dake dakin karatu na Obasanjo da safiyar yau."A matsayinka na tsohon ministan harkokin kasashen waje Sule kasan duniya, ka zagaya duniya kuma kasan yadda za'a yi mu'amula da k'asashen duniya, nayi murna da farin ciki da abinda na gani a Jigawa a lokacin da kake matsayin Gwamna, ba shakka kayi duk abinda ya dace ace anyi. Inji Obasanjo.

"Sule kana da sadaukarwsadaukarwa, tunani, gogewa, zummar yiwa mutane aiki, Dan haka zaka iya kuma zaka yi abinda ake buk'atar ayi wa Nijeriya".

A jawabinsa Sule Lamido ya bayyana ziyarar da cewa ba ziyarace ta neman suna ko wani abu daban ba domin babu abinda baka Sani ba a kaina (Obasanjo) asali ma kafi kowa sanin waye ni, na ziyarce ka domin naga lafiyarka, na gaisar da kai, na Mama bayanin yadda ake tafiya da kuma neman fatan alheri da adduo'i da kuma shawararka a matsayinka na Uba.
rariya.

No comments:

Post a Comment