Sunday, 26 August 2018

TA LEKO TA KOMA: Gwamnati Ta Musanta Karin Alawus Ga Masu Yiwa Kasa Hidima

Gwamnatin tarayya ta karyata rahotannin cewa ta kara alawus alawus din da take baiwa masu yiwa kasa hidima ( NYSC) daga N19,8000 zuwa N48,900 a kowane wata. 


Ministan Kwadago, Chris Ngige ya ce, ba bu yadda gwamnati za ta yi karin alawus din ba tare da ta yi karin albashin ma'aikatan gwamnati ba inda ya jaddada cewa har yanzu majalisar ministoci ba ta karbi wani bukata na karin alawus din ba.

No comments:

Post a Comment