Friday, 31 August 2018

Tambuwal zai tsaya takarar shugaban kasa

Gwamnan ihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya yanki tikitin neman tsaya wa takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar PDP a babban zaben badi.


Da yammacin ranar Alhamis ne gwamnan ya karbi fom din a ofishin jam'iyyar PDP a Abuja.

Tambuwal ne mutum na biyu da ya ayyana aniyyarsa ta yin takarar ranar Alhamis, bayan tun da farko Shugaban Majalisar Dattawan kasar Abubakar Bukola Saraki ya ce zai tsaya takarar.

A ranar Laraba ne tsohon gwamnan Kano Satanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi gangamin kaddamar da takararsa a Abuja.

Aminu Tambuwal dai yana yin wa'adinsa ne na farko a matsayin gwamnan jihar Sakkwato, wanda aka zabe shi a shekarar 2015.

Gwamnan na Sakkwato yana daga cikin manyan 'yan siyasar kasar da suka fice daga APC zuwa PDP a watan Yuli.

Wasu dai na ganin bukatar takarar shugabancin kasar ce ta fitar da shi daga APC, kasancewar ba zai yi samunta a jam'iyyar ba, bayan da Shugaba Buhari ya nuna aniyyarsa ta yin takara a karo na biyu.

To sai dai gwamnan ya ce ya bar jam'iyyar ne saboda gwamnatin Buhari ba ta yi wa jiharsa komai ba.

Akwai dai mutane da dama da suka nuna aniyyarsu ta tsayawa takara a jam'iyyar ta PDP, kuma hakan ta sa ake ganin za a fafata sosai a zaben fidda gwani na jam'iyyar.


No comments:

Post a Comment