Thursday, 9 August 2018

Thibaut Courtois ya koma Madrid, Navas yace shi da Madrid mutu ka raba, Chelsea ta sayi golan Atletico Bilbao

A yayin da kasuwar cinikin 'yan wasan kwallon kafa ta kulle a yau,Tsohon  Golan Chelsea, Thibaut Courtois ya koma bugawa kungiyar Real Madrid wasa akan akan yarjejeniyar shekaru shida.


Wannan dalili yasa aka fara rade-radin cewa Golan Madrid Keylor Navas zai bar kungiyar tunda gashi ta sayi sabon gola.

Saidai da yake mayar da martani akan wancan rade-radin, Navas yace bashi da niyyar barin Madrid, idan ina son barin Madrid to ina son mutuwata, injishi, kamar yanda Goal ta ruwaito.

Bayan tafiyar Thibaut, Chelsea ta sayi golan Atletico Bilbao.

Chelsea ta sa yi Kepa Arrizabalaga daga Athletic Bilbao kan kudi fan miliyan 71 - kudi mafi yawa da aka taba kashewa wajen sayen gola, kuma kudi mafi yawa da kulob din ya taba kashewa.

Kepa, mai shekara 23, zai isa Stamford Bridge bayan an cimma sharadin fansa cikin yarjejeniyarsa .

No comments:

Post a Comment