Monday, 20 August 2018

Tinubu Ya Taba Gulmata Mani Bai Son Salon Mulkin Buhari>>Bukola Saraki

Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya yi raddi ga Tsohon Gwamnan Legas, Bola Tinubu inda ya nuna cewa rashin tuntubarsa kan muhimman batutuwan da suka shafi kasa da gwamnatin Buhari ke yi, ya tilasta shi komawa PDP.


Ya ce, duk wadanda suka taka rawa wajen kafa gwamnatin APC wanda ya hada da mutanen jiharsa ta Kwara duk an yi watsi da su yana mai cewa, Buhari ya kan rubutowa majalisar ce kan wata bukatarsa wanda ya kamata ya fara tuntubar majalisar kafin ya rubuto.

Ya kara da cewa, ya kai wannan korafin ga shugabannin APC wanda ya hada har da Bola Tinubu wanda shi kansa ya taba nuna masa cewa ba ya son salon mulkin Buhari amma daga baya ya fahinci cewa tsohon Gwamnan Legas din na son cimma burinsa ne na zama Shugaban kasa idan wa'adin Buhari na biyu ya cika a shekarar 2023.
Rariya.

No comments:

Post a Comment