Tuesday, 28 August 2018

Tottenham ta lallasa Manchester united da ci 3

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta yi wa kungiyar Manchester united dukan tsiya inda ta lallasa ta da ci 3 – 0.


Dan wasan Tottenham Lucas Moura ne ya zura kwallaye biyu a ragar United sannan Harry Kane ya saka kwallo daya.

Manchester ta yi kokarin ta farke ko da kwallo daye ne amma wankin hula a wannan karon ya wuce dare sai da ya kai su har safiya kuma ba a cimma buri ba.

An buga wasanni uku kenan da fara wasan Firemiya lik, amma wasa daya ne tak Manchester united ta samu nasara a kai.
Premiumtimeshausa.

No comments:

Post a Comment