Sunday, 26 August 2018

Trump na da ɗa 'shege'

A ranar Asabar din nan da ta gabata,kafar yada labarai ta Amurka CNN ta ce ta gano wasu takardu,wadanda ke tabbatar da kasancewar wani ɗan 'zina' da Trump ya samu daga wata 'yar wanke-wanke.


Wanda ya fara fasa kwai kan wannan lamarin shi ne, tsohon mai gadin benen Donald Trump (Trump Tower).

A takardun,lauyan mai-gadi Dino Sajudin,Marc Held ya ce a baya kwastomansa ya rattaba hannu a wata takarda da kafar yada labarai ta "AMI",wacce ke tirsasa shi kin bai wa wasu kafofi na daban wannan labarin.

Held ya tabbatar da cewa Sajudin ya cika alkawarinsa bayan da aka ba shi dalar Amurka dubu 30,000 a lokacin da AMI ta fara fallasa sirrin.

A cewar wani sharadi da aka gindiya,Sajudin zai biya dalar Amurka milyan 1,000,000,idan har ya yi wancakali da yarjejeniyar da aka shi ko kuma ya ki cika alkawari.

Amma lauya Held ya ce,Sajudin ya yi nasarar 'yantar da kansa ta hanyar soke wannan yarjejeniyar.

Takardun da CNN ta samu na nuna cewa, Sajudin ya kulla yarjejeniya da AMI a watan Nuwamban shekarar 2015.

Kawo yanzu Fadar White House ba ta ce uffan ba game wannan batun.

A 'yan kwanakin nan ma, tsohon lauyan Trump, Michael Cohen ya sanar da cewa, Donald Trump ya bai wasu mata biyu,wadanda suka hada da 'yar fim din batsa Stormy Daniels da kuma mai tallar tufafi,Karen McDougal,wadanda dukannin su ke ikirarin cewa sun taba yin lalata da shugaban na Amurka, toshiyar baki.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment