Monday, 27 August 2018

Tsaffin hadimam gwamnan jihar Skkwato 300 sun jaddada goyon bayansu ga shugaba Buhari

Tsofaffin mataimaka na musamman ga Gwamna Aminu Tambuwal su 300 sun jaddada goyon bayan su ga Shugaba Buhari da Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da Jam'iyyar APC a wata ziyarar barka da Sallah da suka kaiwa Sanata Wamakko jiya a gidansa dake Sokoto. A kwanannan ne masu yiwa gwamnan hidima suka ajiye aikinsu a wani mataki na nuna kin amincewa da canja shekar da gwamna Tambuwal yayi daga jam'iyya me mulki ta APC zuwa babar jam'iyyar adawa ta PDP.


No comments:

Post a Comment